Kimanin daliba daya ce ta gamu da ajalinta, yayin da karin wasu daliban suka samu raunuka daban-daban, sakamakon ruftawar ajin karatu a kan daliban makarantar Government Girls Technical College (GGTC), da ke Potiskum, a jihar Yobe, yau Alhamis.
Wasu ganau bayan faruwar al’amarin, sun shaida wa LEADERSHIP Hausa cewa, ginin ajin ya rikito kan daliban ne sa’ilin da suke tsaka da daukar darasi a makarantar.
- An Jinjinawa Kwarewar Sin A Bikin Nune-Nunen Ayyukan Gona Na Cote d’Ivoire
- Sin Ta Tabbatar Da Goyon Bayanta Ga Kafa Kasashe Biyu Ga Isra’ila Da Palasdinu
Yanzu haka gawar daya dalibar tare da sauran daliban 5 wadanda suka samu raunuka su na kwance a Asibitin Kwararru dake garin Potiskum.
Duk kokarin jin ta bakin shugabar makarantar, kwamishinan ma’aikatar ilimin Firamare da Sakandire a jihar Yobe ya ci tura.
Cikakken labari ya na tafe.