Gwamnan jihar Delta, Rt. Hon. Sheriff Oborevwori ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.
An sanar da sauya shekar ne bayan wani taron sirri da aka yi a ranar Laraba a gidan gwamnati da ke Asaba ta hannun babban sakataren yada labaran gwamnan, Sir Festus Ahon.
- Sin Za Ta Harba Kumbon ‘Yan Sama-Jannati Na Shenzhou-20
- Sabbin Haraji: Yadda ‘Yan Bindiga Ke Tilasta Wa Jama’a Biyan Miliyoyin Kuɗi A Zamfara
Ahon ya ce, matakin da gwamnan ya dauka na sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki ya biyo bayan tattaunawa sosai da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa, da nufin samar da ci gaba mai dorewa ga jihar Delta.
Gwamna Oborevwori, wanda ya samu nasara a zaben gwamna na 2023 a karkashin jam’iyyar PDP, ya samu tarba daga manyan jami’an APC.