Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya kai ziyarar jaje ga Gwamnatin Kano, da iyalan mafarauta 16 da ɓata gari suka kone su har lahira a garin Uromi, da ke Jihar Edo, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a fadin ƙasar nan inda jama’a ke buƙatar adalci ga mamatan.
Da yake jawabi a gidan gwamnatin Kano, Gwamna Okpebholo, ya nuna matuƙar kaɗuwa da lamarin, inda ya bayyana cewa mutane 14 daga cikin waɗanda ake zargi da aikata kisan sun shiga hannu, tare da bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwuiwa ba wajen tabbatar da adalci ga iyalan mamatan.
- Shugaban Ohanaeze Ya Yi Allah-Wadai Da Kisan Ƴan Arewa 16 A Edo
- Kashe Matafiya: Gwamnatin Kano Ta Aika Tawaga Zuwa Edo
A nasa ɓangaren, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya buƙaci Gwamnan Edo, da ya tabbatar an hukunta waɗanda suka aikata wannan aika-aika, ya na mai cewa dole ne a bi doka da oda domin tabbatar da cewa makamancin haka bai sake faruwa ba a ko’ina a ƙasar nan.
Gwamna Yusuf, ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta bayyana sunaye da fuskokin mutanen da aka kama dangane da kisan gillar, wanda a cewarsa hakan zai hana sake afkuwar irin wannan danyen aiki a gaba.
Daga karshe, Gwamnan Kano ya bukaci Gwamnatin Edo, da ta tabbatar an biya diyya ga iyalan mamatan domin rage raÉ—aÉ—in wannan mummunan lamari da ya girgiza same su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp