Sakamakon da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta sanar na zaben ‘yan majalisun dokokin Jihar Yobe, ya nuna dan takarar jam’iyyar PDP, Musa Lawan Majakura ya lallasa na jam’iyyar APC, wanda shi ne kakakin majalisar dokokin jihar, Hon. Ahmed Lawan Mirwa a mazabar Nguru ta waje.
Sakamakon ya nuna jam’iyyar PDP ta samu kuri’u 6648 yayin da ita kuma jam’iyyar APC ta samu kuri’u 6466 a zaben, wanda hakan ya bai wa dan takarar jam’iyyar PDP nasara da kuri’u 182 kan abokin fafatawarsa a zaben.
- Mahara Sun Harbi Ma’aikaciyar INEC A Kuros Riba
- Da Dumi-Dumi: Mace Ta Kayar Da Kakakin Majalisar Filato Da Tazara Mai Yawa
A wannan zaben, Hon. Majakura na PDP ya lallasa Hon. Ahmed Mirwa ne bayan da ya kwashe shekaru 20 ya na jan zarensa a kujerar, daga 2003 zuwa wannan lokacin inda shi ne Kakakin majalisar jihar Yobe daga 2019 zuwa 2023.
A hannu guda kuma, can ma a karamar hukumar Bade ta tsakiya (Bade Central), dan takarar jam’iyyar PDP, Hon. Saddiq Yahaya Attajiri ne ya kwace kujerar dan majalisar APC, Hon. Mohammed Kabiru Maimota, a zaben da ya gudana ranar Asabar.
A sakamakon zaben da hukumar INEC ta rattabawa hannu, ya ayyana dan takarar jam’iyyar PDP ta samu kuri’u 12,863, inda na jam’iyyar APC, ya samu kuri’u 11,248 a zaben, al’amarin da ya bai wa dan takarar jam’iyyar PDP nasara a zaben.