Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da mayar da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) zuwa ofishin Mataimakin Shugaban Kasa domin samun cikakken kulawa kan dokokin da aka kafa su daban-daban.
Shugaban ya amince da wani sabon tsari a hukumance ga ofishin mataimakin shugaban kasa ya kuma sake amincewa da wani adadin mutane da za su taimaka kan harkokin gudanarwa da za su yi aiki tare da mataimakin shugaban kasa wajen sauke nauyin da ke kansa.
Cikakken labarai na zuwa daga baya…