Tsohon gwamnan jihar Anambra, Chinwoke Mbadinuju ya rasu.
Ya rasu yana da shekaru 78 a safiyar Talata a babban asibitin kasa na Abuja bayan gajeruwar rashin lafiya.
Wani makusancin gwamnan ne Cheta Mbadinuju ya sanar da mutuwar. Mbadinuju ya kasance gwamnan Anambra daga 1999 zuwa 2003.