Hankalin ‘yan wasa, ‘yan kallo da makwabta ya tashi a ranar Talata, biyo bayan fashewar tukunyar gas da ta afku a harabar filin wasanni na Alake – daya daga cikin wuraren da ake gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta kasa da ke gudana a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
Duk da cewa, ba a fitar da cikakken bayanin fashewar ba har zuwa hada wannan rahoton, LEADERSHIP ta tattaro cewa, wata motar rarraba iskar gas ce ta kama da wuta yayin da take samar da iskar Gas ga sashen da ke samar da hasken wutar lantarki a filin wasannin.
Fashewar, ta haifar da firgici a tsakanin ‘yan wasa da ‘yan kallo da ke wurin, wadanda suka yi tsere don tsira da rayuwar su.
Cikakkue bayanai daga baya…