Kwana 34 suka rage akan karagar mulki, gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya rantsar da sabbin alkalai 15 da ya nada a kotunan jihar daban-daban a ranar Talata.
Wadanda aka rantsar sun hada da alkalan babbar kotun jihar guda bakwai, da na kotun daukaka kara na shari’a biyar (Khadis), da kuma alkalan kotun daukaka kara guda uku.
Alkalan babbar kotun sun hada da Bashir Shitu Yusuf, Yakubu Badamasi, Abdullahi Isyaka, Joyce Asabe Aka’ahs, Nana Fatima Muhammad, Ambi John Aku da Buhari Mohammed Balarabe.
Wadanda aka rantsar da su a matsayin alkalan kotun daukaka kara ta Shari’a sune; Aminu Ahmad Jumare, Nuhu Mahmud, Murtala Nasir, Abdulrahman Ibrahim da Suraj Mahadi Mohammad
Alkalan kotun daukaka kara sun hada da; Dorothy Sim Inwulale, Dorcas Thabita Antung da Yusuf Yakubu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp