Wata uwar girki, mai sana’ar dafa abinci a Nijeriya, Hilda Effiong Bassey, wacce aka fi sani da Hilda Baci, na shirin karya kundin tarihin duniya na Guinness a gasar girki mafi dadewa da wani mutum ya taÉ“a yi.
Ta samu wannan nasarar ne bayan da ta zarce sa’o’i 87 da mintuna 45 da Lata Tondon ta Indiya ta kafa a shekarar 2019.
Hilda, wacce ta fara gasar a ranar Alhamis da karfe 4 na yamma lokacin da ta daura sanwar girkinta, ta ci gaba da yin girki har na tsawon a kalla sa’o’i 96.
Taron wanda ke gudana a Amore Gardens da ke Lekki, Legas, an yada gasar ne kai tsaye a manhajar YouTube.
Tuni dai, shugaban kasa Muhammadu Buhari da mai jiran gado Bola Ahmad Tinubu suka fara taya Baci murnar samun wannan nasara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp