Asusun kula yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya bayyana cewa sama da yara miliyan 2.9 a Nijeriya ke fama da rashin abinci mai inganci.
Wakiliyar UNICEF a Nijeriya, Misis Cristian Munduate, ta bayyana haka a Ilorin, babban birnin Jihar Kwara, ta bayyana cewa dole ne a kai yaran da abin ya shafa zuwa asibiti domin samun kulawar gaggawa don guje wa mutuwar far-daya.
- Tsokaci Kan Yadda Wasu Matasa Ke Yin Aure Ba Tare Da Sana’a Ba
- Ta Yaya Kasashe Masu Tasowa Za Su Iya Tinkarar Yakin Haraji Da Amurka Ta Tayar?
Cristian Munduate bayyana hakan ne a a lokacin kaddamar da shirin samar da abinci mai gina jiki 40,000, ta amfani da asusun yara na Majalisar Dinkin Duniya. Ya kara da cewa fiye da kashi 40 cikin 100 na yaran a Jihar Kwara suna fama da wannan matsalar.
Wakiliyar UNICEF ta ce gwamnatin Jihar Kwara ta bayar da dala 100,000 ga asusun samar wa yara abinci mai gina jiki, tana mai lura cewa UNICEF ta kawo irin wannan kudade wanda adadinsu ya kai na dala 100,000.
Ta ce, “Daga bayanan da muka samu, yara 2.9 a Nijeriya na fama da rashin abinci mai gina jiki, wannan ba abun ci gaba ba ne. Don haka, ra’ayina shi ne a dauki yaran da abin ya shafa nan take zuwa asibiti don samun kulawar lafiya da gaggawa domin hana mutuwa a kan lokaci.
UNICEF ta gabatar da asusun abinci na yara don karfafa zuba jari a cikin manufofi da shirye-shirye. UNICEF ta jajirce wajen yin hadin gwiwa da gwamnatin Jihar Kwara don yaki da rashin abinci mai gina jiki, musamman a lokacin kwana 1000 na farko na rayuwar yara.
“Kalubalen shi ne, yawan yara fiye da kashi 40 cikin 100 suna da gwannan matsala kuma kusan yara 300,000 suna fuskantar samun kulawar gaggawa don magance wadannan matsaloli.”
Ta danganta dalilan rashin abinci mai gina jiki ga sakamakon talauci, canjin yanayi, rashin samun abinci, da kuma matsalolin tsaro.
A nasa jawabin, Gwamna Jihar Kwara, AbdulRaman AbdulRazak, wanda ya samu wakilcin Sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Jubril Shaaba Mamman, ya bayyana cewa, tasiri mai kyau game da rayuwar yara na Jihar Kwara shi ne, samun abinci mai gina jiki, wanda wannan ya sa aka yanke shawarar karbar shirin asusun samar da abinci mai gina jiki ga yara na UNICEF.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp