A farkon wannan mako ne aka kaddamar da shirin sada zumunta tsakanin yaran Sin da na kasashen nahiyar Afrika inda yara 35 daga kasashen Namibia, da Afirka ta Kudu, da Somaliya, da Uganda, da Afirka ta Tsakiya, da iyayensu suka hadu da takwarorinsu na kasar Sin.
Babban abun dake haifar da sabani da nuna wariya da ma rikici tsakanin al’ummomi a yawancin lokauta, shi ne rashin fahimta da gadon sabani ko takkadama daga zuri’a zuwa zuri’a.
Zancen da ake cewa yara su ne manyan gobe, tabbas ba karya ba ne. Domin a nan gaba kadan, yaran su ne za su ja ragamar kasashenmu da ma duniyar, don haka ya zama wajibi tun suna kanana su yi mu’amala, su fahimci juna su gane bambamce-bambancen dake akwai tsakaninsu, su amince da su tare da girmama juna, lamarin da zai ka ga wanzar da zaman lafiya da jituwa da kuma girmama juna.
Cikin kwanaki 6 da shirin zai dauka, yaran za su kai ziyara fadar sarakuna ta Sin wato Forbidden City a Beijing, da gidan adana kayayyakin kimiyya da fasaha na lardin Henan, da gidan adana kayayyakin tarihi na Rawayen kogi da sauransu, don kara sada zumunta ta hanyar yin karatu da mu’amala da juna. Wato ba mu’amala da takwarorinsu kadai za su yi ba, har ma da ziyartar wurare daban daban, inda za su ga sassan kasar Sin zahiran da idanunsu. Tabbas bayan komawar wadannan yara, za su samu wani ra’ayi na su don gane da kasar Sin, wanda babu wanda zai iya gogewa, haka kuma za su bayar da labari ga takwarorinsu, a sannan kuma wannan fahimta da ra’ayi za ta yadu a tsakaninsu.
Idan har wannan shiri ya dore, to nan bada dadewa ba, al’ummomin bangarorin biyu za su kasance tamkar ‘yan uwa na jini, haka kuma yaran za su kai ga tabbatar da burin Sin na samun al’ummar Sin da Afrika mai makoma ta daya. Shi ya sa ba zan taba daina jinjinawa hangen nesa irin na kasar Sin ba. Hakika wannan yunkuri zai taka rawa wajen kawar da sabani da kyama da karyata jita jita da kuma wanzar da zaman lafiya kamar yadda ake fata. (Fa’iza Mustapha)