An bayyana tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari a matsayin wanda ya lashe zaben Sanatan Zamfara ta Yamma a zaben da aka kammala a ranar Asabar.
Jami’in tattara bayanai na yankin Zamfara ta Yamma, Farfesa Rufus Teniola na Jami’ar Tarayya da ke Gusau, ya bayyana Abdulaziz Yari a matsayin wanda ya lashe zaben da jimillar kuri’u 147,346 inda ya doke abokin hamayyarsa, Bello Fagon na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 55,083.
- Kwankwaso Ya Lashe Kano, Ya Bai Wa Tinubu Da Atiku Gagarumar Tazara
- Tawagar Masu Aikin Jinya Ta Kasar Sin Dake Kasar Togo Ta Yi Aikin Jinya Kyauta
Yayin da dan takarar jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u 363 sannan dan takarar jam’iyyar Labour ya samu kuri’u 111.
Haka zalika, an bayyana dan takarar jam’iyyar APC a mazabar tarayya ta Anka/Talata Mafara Muhammad Isah Anka a matsayin wanda ya lashe zaben.
Da yake sanar da sakamakon zaben, jami’in zaben mazabar na INEC, Farfesa Ibrahim Garba na Jami’ar Tarayya ta Gusau ya bayyana sakamakon kamar haka;
Yusuf Kabiru na AA 47, Bashar Nafaru na ADC 147, Ayuba Shamsudeen na ADP 106, Muhammad Isah Anka na APC 47,722, Mustapha Suleiman na NNPP 130.
Sauran sun hada da Aliyu Sani na NRM da kuri’u 84, Kabiru Yahaya na PDP ya samu kuri’u 14,872, Aminu Same daga SDP 45 yayin da Lawal Umma na YPP ya samu kuri’u 40.