A baya-bayan nan mambobin hukumar kula da cinikayya ta duniya WTO, suka yi nasarar kammala tattaunawa game da kunshin yarjejeniyar saukaka zuba jari.
Da take tsokaci kan hakan, kakakin ma’aikatar kula da cinikayya ta kasar Sin madam Shu Jueting, ta bayyana a yau cewa, nasarar kammala tattaunawa da ma ciimma daidaito kan yarjejniyar saukaka zuba jarin sun nuna cewa, duk da dimbin kalubalen da dunkulewar tattalin arzikin duniya ke fuskanta, mambobin WTO za su iya hada kai wajen tunkarar kalubalen duniya, kuma ka’idojin cinikayya tsakanin bangarori da dama na iya tafiya da yanayin da ake ciki, kana za a iya tunkarar abubuwan da ake hasashe da ma bukatun ‘yan kasuwa.
Yarjejeniyar saukaka zuba jarin wadda ita ce irinta ta farko a duniya da ta shafi batun zuba jari, na da nufin tabbatar da gaskiya a manufofin kasashe na zuba jari, da saukaka matakan amincewa zuba jari da karfafa hadin kan kasashen duniya a bangaren da saukaka kwarar jari a duniya ba tare da tangarda ba.
Bisa kiyasin cibiyoyi masu ruwa da tsaki, idan aka yi nasarar aiwatar da wannan yarjejeniya, za ta iya kawo dalar Amurka triliyan 1 ga ci gaban tattalin arzikin duniya. (Fa’iza Mustapha)