A yau Litinin ne ake sa ran Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya (ASUU), zata yi taron gaggawa domin cim-ma matsaya kan sake tsunduma yajin aiki kan zaftare albashin watan Oktoba da Gwamnatin Tarayya ta biya mambobinta.
Aminiya ta rawaito cewa, Majalisar Zartarwa (NEC) ta ASUU ta kira taron ne a daidai lokacin da Gwamnatin Tarayya ke shirin biyan albashin wata taskwas ga malaman jami’a da suka balle daga ASUU, wadda ta shafe wata takwas tana yajin aiki a baya.
- Malaman Jami’o’i Sun Koma Bakin Aiki Cikin Yunwa – Shugaban ASUU
- Yajin Aikin ASUU: Gwamnatin Kwara Ta Samar Da Motoci Kyauta Don Jigilar Dalibai
Aminiya ta ruwaito wani jami’in ASUU da ya nemi a boye sunansa, yana cewa, “NEC din ASUU za ta yi zama a ranar Litinin 7 ga Nuwamba don cim-ma matsaya kan shiga sabon yajin aiki, saboda rabin albashin da aka biya mu a Oktoba.
“ASUU ta fusata da abin da Gwamnatin Tarayya ta yi, don haka za ta yanke shawara a ranar 7 ga watan Nuwamba,” in ji shi ta wayar tarho a karshen mako.
Kungiyar ta kira taron gaggawan ne kasa da wata guda bayan janye yajin aikin da ta yi wata takwas tana gudanarwa daga 14 ga Fabrairu zuwa 14 ga Oktoba, 2022.
Da yake magana game da zaman, wanda zai gudana a Jami’ar Abuja, wani dan kwamitin zartarwar ASUU ya ce yanke albashin ya fusata malaman jami’a kuma suna zargin Ministan Kwadago, Chris Ngige, ne ya sa aka yanke.