Baya ga ayyukan ta’addanci da haduran mota da ke cin rayukan dimbin al’umma, yawaitar hadurran jiragen kwale- kwale ne mafi lakume rayukan al’umma a yankin Arewa.
Yankin Arewa ne a sahun gaba wajen yawaitar hadurran jiragen kwale- kwale a kasar nan ta yadda a lokaci zuwa lokaci a kan samu asarar rayuka da dukiyoyi a dalilin haduran jiragen ruwa musamman a yankin da har yanzu ke amfani da kwale- kwale a matsayin hanyar sufuri.
- Sanata Wadada Ya Fice Daga Jam’iyyar SDP Bayan Ganawa Da Tinubu
- EFCC Na Neman Surukin Atiku Abubakar Ruwa A Jallo
Galibi ‘yan kasuwa da manoma a kauyuka da dama kan dogara kacokam wajen amfani da hanyoyin sufurin jiragen ruwa wajen zuwa kasuwanni da gonaki lamarin da ke jefa rayukan su a cikin hadari.
A kan wannan jama’a na ci- gaba da nuna damuwa yadda ake samun yawaitar hadurran kwale-kwale a yankin Arewa da ke cin rayukan dimbin al’umma ba tare da shawo kan matsalar ba.
Kasawar gwamnatoci wajen samar da hanyoyin mota da hada kauyuka da gadoji ne dalilin da yasa garuruwa da dama ba su da zabi face amfani da jiragen ruwa musamman na katako wajen sufuri ta hanyar jefa rayukan su a cikin hatsari.
A kowace shekara a kan samu hadurran jiragen kwale- kwale da dama wadanda galibi daruruwan al’umma kan rasa rayukan su bisa ga sakaci da yi wa jirgi lodin da ya wuce kima.
Jihohi 28 ne ke da manyan kogunan da ke da alaka da juna a fadin kasar nan wadanda ke da tsawon sama da kilimita dubu 10, kuma suna karuwa da tsawon kilomita dubu 3, 800 a kowace shekara kamar yadda hukumar kula da hanyoyin ruwa ta bayyana.
Kididdiga daga hukumar bincike da kiyaye hadurra (NSIB) ta bayyana cewar fiye da kashi biyu bisa uku na hadurran da ake samu a jiragen ruwa kan faru ne a dalilin nutsewa da mutane ke yi saboda rashin amfani da rigar kariya.
Rashin kulawa da jiragen kwale- kwalen da rashin kiyaye dokoki, da rashin saka rigunan kariya na daga cikin abubuwan da ke taimakawa wajen haddasa hadurran jiragen ruwa a Arewa.
Rashin kyawo ko tsaftar kogunan da ake da su a kasar nan manyan matsaloli ne da ke haddasa hadarin jiragen ruwa a bisa ga yadda tarkace ya yi yawa a cikin koguna.
A ire- iren hadurran kwale-kwalen jama’a da dama kan ji raunuka, wasu kan fita hayyacin su, a kan kasa gano wasu a yayin da wasu kan yi bankwana da duniya bakidaya ba tare da ceton rayukan su ba.
Mahukunta kan sha alwashin daukar kwararan matakai domin shawo kan aukuwar hadurran ko magance mace- macen amma alwashin a fatar baki ne kawa domin bai tabbata ba.
A wata tattanawa da manema labarai, Farfesa Bello Bada wanda ke sharhi kan al’amurran yau da kullum ya bayyana cewar amfani da tofaffin jiragen ruwa na daga cikin abubuwan da ke haifar da yawaitar hadarin kwale- kwale.
Ya ce daukar mutane da kaya fiye da kima babbar matsala ce da ke haddasa hadurran jiragen ruwa a kasar nan wanda ya kamata a kiyaye.
Domin kiyaye rayukan al’umma, Shehin Malamin ya ce ya wajaba mahukunta su rika sa ido domin tabbatar da jama’a na amfani da kwale- kwalen da ya dace tare da daukar mutane da kayan da suka dace.
A mafi yawan garuruwan da koguna da hanyoyin ruwa suke, jiragen ruwa ne hanyar sufurin su amma kuma zirga- zirgar su na zama cikin hadari kamar yadda ake gani a bisa ga yawaitar hadurra da asarar rayuka.
A kwanan nan hankalin al’umma da hukumomi ya karkata a yayin da jirgin kwale-kwale ya nutse da mutane sama da 50 a kogin Goronyo da ke Sakkwato.
Jirgin wanda ya dauko fasinjojin da kayan su da suka hada da babura suna kan hanyar zuwa kasuwar mako ta karamar hukumar Goronyo a yayin da ya kife da su a kauyen Kojiyo da misalin karfe 1:30 na ranar Lahadi a makon jiya.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA ta bayyana cewar ta tura jami’an ta a Sakkwato jim kadan da faruwar lamarin domin bayar da agajin gaggawa na ceto mutanen kamar yadda shugabar hukumar Zubaida Umar ta bayyana.
Sai dai zuwa lokacin hada wannan rahoton an samu nasarar ceto mutane 26 daga ruwan. Haka ma zuwa yammacin Talata an samu nasarar gano gawar mutane uku da suka rasa rayukan su.
Dan majalisar wakilai da ke wakiltar mazabar Gada/Goronyo, Honarabul Bashir Usman Gorau a tattaunawar sa da manema labarai ya tabbatar da ceto mutane 26 tare da cewar adadin mutane 40 zuwa 50 da ake yadawa sun salwanta hasashe ne kawai amma babu tabbacin adadin mutanen da suke a cikin jirgin.
Ya ce an samu cikakken hadin kan hukumar kula da kogin Rima a karkashin jagorancin Alhaji Abubakar Malam wajen rufe ruwan dam domin ci-gaba da bincike a kokarin ceto mutanen wadanda ya ce sarakunan ruwa na iyakar kokarin su domin ganin sun cero mutanen tare da cewar ya zama wajibi a dauki kwararan matakai domin hana afkuwar hakan a gaba.
A yayin da gwamnatin Sakkwato ke jajantawa iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, gwamnatin ta bayar da gudunmuwar naira miliyan 20 da buhun abinci 100 domin tallafawa iyalan wadanda suka rasu.
Mataimakin Gwamnan Sakkwato, Idris Gobir wanda ya kai ziyarar jajantawar ya kuma bayyana cewar gwamnatin jiha za ta yi gaggawar kammala aikin gadar da take kan yi a yankin domin saukaka harkokin sufuri.
Ya ce haka ma suna kokarin siyo jiragen ruwa na zamani masu amfani da injin da rigunan kariya domin rabawa al’umma a kananan hukumomi shida da ke da albarkar ruwa domin magance aukuwar hadarin a nan gaba.
Idan aka yi waiwayen baya, a watan Satumba 2024, gwamnatin jihar Sakkwato ta bayyana cewar za ta siyo jiragen ruwa na zamani da rigunan kariya na naira bilyan 1 da miliyan 100 domin rabawa ga kananan hukumomi 22 cikin 23 da suka fuskanci ambaliyar ruwa,.
Sai dai har zuwa yau shekara daya da aminta da bayar da kwangilar ba a sake jin batun labarin kwangilar ba wadda Kwamishinan Kananan Hukumomi, Dadi Adare ya bayyanawa manema labarai a sakamakon zaman majalisar zartaswar gwamnatin jiha da Gwamna Ahmed Aliyu ya jagoranta
A shekarar 2024 kadai an samu asarar rayuka sama da 400 a tsakanin watan Yuli da Disamba 2024 kawai wadanda suka faru a dalilin rashin kwarewa da rashin amfani da matakan kariyar sufurin ruwa.
A Disamba 2024, an gano mutane 54 a yayin da jirgin kwale- kwale ya kife dauke da mutane sama da 200 a Kogin Neja. Wata daya gabanin sa kuwa, mutane kusan 300 ne suka nutse a jirgin katako a tsakiya Neja tare da kashe mutane kusan 200.
A wani hadarin da ya dauki hankalin al’umma, mutane sama da 100 ne suka bakunci lahira a yayin da jirgin ruwa ya nutse da su ba tare da samun ceto ba.
Jirgin da matafiyan ke ciki yana dauke ne da kusan mutane 300 da ke tafiya daga Kwara zuwa jihar Neja bayan kammala hidimar aure.
A Yuni 2025, jirgin kwale-kwale ya yi mummunan hatsari tare da nutsewa da rayukan mutane 37 a kogin Gbajiibo a jihar Neja dauke da mutanen jihar Kwara.
A Disamba 2024, mutane 20 sun rasa rayukan su a Kogin Benue a yayin da jirgin kwale-kwale ya kife da su a kusa da kauyen Ochalanya a karamar hukumar Agatu da ke Benue a kan hanyar su ta komawa jihar Nasarawa.
A Yuli 2025, wani jirgin ruwa dauke da fasinjoji 39 da kayan su ya nutse da su a cikin ruwa a Shiroro da ke jihar Neja, sai dai an samu nasarar ceto mutane 26, a yayin da 13 suka rasa rai.
Shugaban Kasa Tinubu ya bayyana cewar gwamnati ba za ta sa idanu ta ci- gaba da ganin rayukan al’umma na tafiya haka kawai ba a bisa ga sakaci ko rashin sani, a cewarsa bin ka’idojijn kiyayewa ba zabi ba ne wajibi ne.
Tinubu ya ce abin damuwa ne yadda hadurran ke ci-gaba da faruwa duk da ilmantarwarwa a kodayaushe da ma’aikatar muhalli, ma’aikatar tattalin arzikin teku da hukumar kula da hanyoyin ruwa ta kasa ke yi.
A kan wannan ya bukaci sarakuna, shugabannin addini da kananan hukumomi da su kara wayar da kan al’umma kan bin ka’idojijn kiyayewa musamman a hanyoyin ruwa, ya ce yana da kyau jama’a su fahimci cewar a na iya kiyaye hasarar rayukan da ake yi.
Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a watan Yuli a bisa ga ambaliyar ruwa a Yola da ke Adamawa da kifewar jirgin kwale-kwale a kauyen Guni da ke jihar Neja
Hukumar kula da hanyoyin jiragen ruwa wadda ke da alhakin kiyaye koguna da hanyoyin ruwa a Nijeriya ta bayyana matakan da ya kamata a dauka domin kiyaye hadurra wadanda suka hada da zirga-zirga a tsakanin shida na safe zuwa shida na yamma a kowace rana, haka ma wajibi ne matukan jiragen ka da su yi lodi ya wuce kima.
Hukumar ta ce matukan jirgin su guji amfani da tsofaffin jirage musamman wadanda suka wuce shekaru biyar, bugu da kari matukan jirgin su guji shan barasa ko kwaya kafin da yayin tuka jirgi haka ma wajibi ne fasinjoji su saka rigar kariya kafin shiga jirgi.
Sauran hanyoyin kariyar da hukumar ta bayyana sun hada da wajibi ne dukkanin jirage da matuka jiragen suna da rajista da hukumar kula da hanyoyin ruwa ta kasa, masu tuka jirgin su rika duba lafiyar jiragen akai- akai haka ma matuka jirgin su rika sanar da fasinjoji matakan kariya.
Kaftin Ahmad Idris masani harkokin sufurin ruwa, ya bayyana cewar babban abin da ke kawo matsalar hadarin jirgin ruwa shine rashin kwarewar matukan jirgin, rashin amfani da hanyoyin kariya, rashin amfani da rigar kariya, yin lodi fiye da kima da rashin kula da lafiyar jirgi.
Ya ce akwai bukatar daukar matakin gaggawa domin magance matsalolin domin samun amincewar jama’a wajen amfani da sufurin hanyoyin ruwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp