Yawan hatsin da kasar Sin ta girbe cikin wa’adin shirin raya kasa na shekaru biyar biyar karo 14 tsakanin shekarar 2021 zuwa ta 2025, ya kai wani sabon matsayi, inda ya zarce tan miliyan 700 a karon farko a bara.
Ministan kula da aikin gona da harkokin karkara Han Jun ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a yau Talata, inda ya ce, adadin ya nuna karuwar tan miliyan 37, idan aka kwatanta da na shekarar 2020.
Wasu alkaluma da aka fitar a hukumance sun alakanta karuwar da aka samu da ingantuwar kayayyakin dake tallafawa aikin gona da kuma fasahohin aikin gona.
Kasar Sin ta samar da sama da kadada miliyan 66.7 na ingantattun gonaki, yayin da ci gaban fasaha ya zama muhimmin abun dake ingiza samun girbi mai armashi, inda gudunmuwar da yake bayarwa ya karu zuwa kaso 63.2.
Haka zalika, kudin shigar manoma yana ta karuwa cikin sauri tun daga shekarar 2021, inda kudin shigar kowannen mutumin kauye ya kai yuan 23,119 kwatankwacin dalar Amurka 3,255 a shekarar 2024. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp