A kwanakin baya ne, kungiyar hadin kan masana’antun kera injuna ta kasar Sin, ta fitar da kididdigar dake nuna cewa, a watanni 6 na farkon bana, yawan karin kudin da aka samu a wannan bangare ya karu da kashi 0.7% bisa na makamancin lokaci na bara, yayin da yawan kudin dake shafar cinikin fitar da injuna zuwa ketare na kasar Sin, ya kai dala biliyan 344.12, wanda ya karu da kashi 10.41%.
Daga cikinsu motoci da injunan injiniya sun kasance a kan gaba.
Tun daga farkon wannan shekara, yankuna da sassa daban-daban na kokarin tinkarar mawuyacin halin da ake ciki da kuma fito da jerin matakai don daidaita ci gaba.
Mataimakin shugaban kungiyar Chen Bin ya bayyana cewa, duk da kalubalen da dama da ake fuskanta, yawan karuwar da aka samu a wannan sha’ani, ya nuna tsayin daka da ci gaban kamfanonin.
A nan gaba kuma, za a gaggauta aiwatar da manufofin tabbatar da bunkasa tattalin arziki don taimakawa kamfanoni da masana’antu wajen magance matsalolinsu. (Amina Xu)