Hukumar kididdiga ta kasar Sin (NBS) ta sanar a yau cewa, a cikin ‘yan shekarun nan, yawan jama’ar kasar Sin na ci gaba da karuwa, kana tsarin samar da aikin yi ya ci gaba da inganta, yayin da yanayin aikin yi shi ma bai sauya ba.
Ya zuwa karshen shekarar 2021, yawan jama’ar kasar Sin, ya kai biliyan 1 da miliyan 412.6, wanda ya karu da miliyan 53.38 kan na karshen shekarar 2012.
A shekarar 2021 kuwa, jimillar ma’aikatan dake birane, ya kai miliyan 467.73, wanda ya karu da miliyan 94.86 a kan shekarar 2012. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)