A yayin taron dandalin tattaunawa game da kirkire-kirkire na Pujiang na 2023 wanda aka gudanar a birnin Shanghai, ’yan jaridu sun samu labarin cewa, jirgin saman dakon fasinja samfurin C919 na farko da kamfanin COMAC ya kera, ya kaddamar da sufurin kasuwanci na farko a ranar 28 ga watan Mayun shekarar bana.
Kawo yanzu, kamfanin COMAC ya samar da jiragen saman fasinja samfurin C919 guda 2 ga kamfanin sufurin fasinja na China Eastern, kana yawan jiragen sama samfurin C919 da aka yi oda ya kai 1061.
Bisa labari daban da aka bayar, an ce, wani jirgin saman fasinja samfurin C919 da kamfanin COMAC na kasar Sin ya kera ya sauka a filin jirgin saman kasa da kasa na Diwopu dake Urumqi, babban birnin jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin a jiya Litinin.
A cewar kamfanin COMAC, saukar jirgin ya kaddamar da gwajinsa da za a yi na tsawon makonni biyu a fadin filayen jiragen sama 25 na jihar Xinjiang.
Bisa shirin da aka yi, kamfanin COMAC zai yi amfani da jirage biyu samfurin C919 wajen gwajin, wanda zai kai su filayen jiragen sama da suka hada da na Karamay da Yining da Kuqa da Altay da sauran manyan filayen jiragen sama na Xinjiang.
Tafiyar jirgin sama shi ne tsarin sufuri mafi sauki tsakanin yankunan jihar Xinjiang, kasancewarta mai fadi da shimfidar kasa mai sarkakiya da kuma tarin filayen jiragen saman fasinja.
Gwajin jirgin na C919, zai taimaka wajen biyan bukatun fasinjoji na tafiya mai inganci da lalubo sabbin hanyoyin tafiyar da harkokin sufurin jiragen saman fasinjoji na cikin gida. (Safiyah Ma, Fa’iza Mustapha)