Hukumar kididdiga ta kasar Sin ta gabatar da alkaluman tattalin arzikin kasar na rabin farko na shekarar bana a yau Talata, inda mataimakin hukumar Sheng Laiyun ya ce, a wa’adin watannin shida, Sin ta aiwatar da manufofi daga manyan fannoni yadda ya kamata, tattalin arzikin kasar ya samu karuwa ba tare da tangarda ba, duk da kalubaloli da mawuyancin halin da ake fuskanta.
An yi kididdigar cewa, yawan GDPn a rabin farko na shekarar bana ya kai fiye da kudin Sin Yuan biliyan 66053, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 9207, wanda ya karu da kashi 5.3% kan na makamancin lokaci na bara.
Alkaluma sun kuma nuna cewa, a wa’adin rabin shekarar ban, yawan kudin dake shafar bangaren sayar da kayayyakin masarufi ya karu da kashi 5% bisa na makamancin lokacin bara, adadin dake bayyana karfin sayayya na kasar. Ban da wannan kuma, a rabin farko na shekarar ta bana, yawan kudaden da daidaikun jama’ar Sin ke iya kashewa ya karu da kashi 5.3%. Dadin dadawa, matsakaicin mizanin yawan rashin aikin yi a birane da garuruwa ya kai kashi 5.2%. Kana, a watan Yuni da ya shude, karuwar darajar masana’antun kasar Sin ta kai kashi 6.8% kan na makamancin lokaci na bara. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp