Yau jami’in sashen kula da inganta sayayya na ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin, ya yi tsokaci kan yanayin sayayya da kasar ta kasance a ciki a watan Agusta.
A watan na Agusta, an gudanar da harkokin sayayya yadda ya kamata. Bisa kididdigar da hukumar kididdigar kasar Sin ta bayar an nuna cewa, yawan kudin da aka kashe wajen cinikin kayayyakin masarufi a watan Agusta ya kai RMB triliyan 3.97, adadin da ya karu da kashe 3.4 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara, saurin karuwar kuma ya karu da kashi 1.3 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara.
Da farko, an samu ci gaban sayayya yadda ya kamata. A watan Agusta, manyan kantunan sayar da kayayyaki irin su kwamfutar hannu, na’urar sanyaya wurare ta zamani, da wayar salula sun samu karuwa mai karfi.
Na biyu, an bullo da abubuwa masu daukar hankali game da sayayya. Karuwar bukatun da ake da su wajen yawon shakatawa da ma motsa jiki a lokacin hutu na zafi ta haifar da saurin karuwar sayayya.
Na uku, an samu saurin ci gaban sayayya masu sabon salo, wadanda suka shafi fannonin fasahar zamani, da marasa gurbata muhalli da kuma kiwon lafiya da dai sauransu.
Na hudu, an yi ta samu ci gaban sayayya sakamakon masu yawon bude ido daga ketare. Bisa ga manufar rage haraji lokacin barin kasa da kasar Sin ke gudanarwa, an shirya shirin “Sayayya a Sin” yadda ya kamata, wanda hakan ya canza fa’idar yawan baki daga ketare da suke yawon shakatawa a kasar zuwa habaka kudin da ake kashewa. (Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp