A shekarar 2024 da ta gabata, yawan kudin da kasar Sin ta zuba kan manyan ababen da ake bukata wajen gudanar da layin dogo ya kai dala biliyan 117, wanda ya karu da kashi 11.3% a kan shekarar 2023, matakin da ya bayyana samun bunkasuwa cikin sauri a wannan bangare, kazalika sabbin layukan dogo da aka gina sun kai kilomita 3113, daga ciki akwai layin jirgin kasa mai saurin tafiya kilomita 2457.
Ya zuwa karshen shekarar 2024, yawan layin dogo da aka yi amfani da su ya kai kilomita dubu 162, daga cikinsu layin jirgin kasa mai saurin tafiya ya kai kilomita dubu 48.
Ban da wannan kuma, yawan hajojin da dukkan layukan jirgen kasa suka yi jigilarsu ya kai ton biliyan 3.99, adadin da ya karu da kashi 1.9% a kan shekarar 2023, hakan ya sa an samu karuwa a cikin shekaru 8 a jere a wannan bangare. (Amina Xu)