Hukumar samar da lantarki ta kasar Sin ta ce jimilar karfin lantarki da tashoshin samar da makamashi mai tsafta da aka kafa a kasar Sin suka samar, ciki har da makamashin iska da rana da na halittu, ta haura kilowatt biliyan 1.27, zuwa karshen watan Agusta.
Wannan adadi kuma, shi ya dauki kaso 40.7 na jimilar lantarkin da kasar ke samarwa.
A cikin watan Agusta, makamashin da ba na albarkatun man fetur ba, shi ya dauki kaso 40 na makamashin da aka yi amfani da shi a kasar. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp