Hukumar kwastan ta birnin Shanghai ta fitar da wata kididdiga a baya-bayan nan, wadda ta nuna cewa, yawan motocin da aka fitar waje a watan Jariaru daga tashar ruwa ta Haitong da ta Nangang, wato muhimman tasoshin ruwa biyu da ake fitar da motoci zuwa ketare a birnin Shanghai, ya kai kusan dubu 110.
Hukumar ta ce, a watan Janairu, yawan motocin da aka fitar waje daga tashar Nangang ya karu da kashi 43% bisa na makamancin lokacin bara. Ban da wannan kuma, daga ranar 18 zuwa 25 ga watan nan da muke ciki wato cikin kwanaki 7 ke nan, yawan motoci masu aiki da tsabaccen makamashi da aka fitar a wannan tashar ya kai kusan dubu 10, kazalika yawan motocin da aka shigar tare da fitarwa daga wannan tashar ya kai kimanin dubu 17. Hakan ya nuna cewa, motocin da Sin ta kera na kara samun karbuwa a ketare. (Amina Xu)