Kididdigar da hukumar kula da musayar kudaden kasar Sin ta bayar a ranar jiya ta nuna cewa, ya zuwa karshen watan Yulin bana, yawan musayar kudaden da aka adana na Sin ya kai dala tiriliyan 3.1041, wanda ya karu da dala biliyan 32.8 bisa karshen watan Yuni, inda ya karu da 1.07%.
A watan Yulin bana, an tafiyar da kasuwar musayar kudaden Sin lami lafiya, kuma samar da musayar kudade a cikin gida yana daidaituwa.
Mataimakiyar shugaba, kana kakakin hukumar kula da musayar kudaden kasa ta Sin Wang Chunying ta bayyana cewa, a halin yanzu yanayin tattalin arzikin kasa da kasa yana fuskantar kalubale, abubuwa na rashin kwanciyar hankali da rashin tabbas suna karuwa, kana kasuwannin hada-hadar kudi na kasa da kasa suna sauyawa. Sin ta yi yaki da cutar COVID-19 kuma ta samu bunkasar zamantakewar al’umma, haka kuma tattalin arzikinta yana da isasshen kuzari, halin da ya shiga na yanayi mai kyau ya kasance cikin dogon lokaci ba tare da sauyawa ba, kuma zai ci gaba da goyon bayan kwanciyar hankalin yawan musayar kudade. (Safiyah Ma)