Jigilar mutane a bikin murnar sabuwar shekara ta kalandar gargajiya ta kasar Sin ya zama aikin bulaguron mutane mafi yawa a duniya a idon kafofin yada labarai na duniya. An fara wannan aiki ne daga ran 26 ga watan Janairu zuwa ran 5 ga watan Maris na bana, wanda zai kwashe kwanaki 40. Hukumar zirga-zirga ta kasar Sin ta yi kiyasin cewa, a cikin wannan lokaci, za a yi bulaguro har sau fiye da biliyan 9, wanda ya ninka na shekarar 2023 sau 2, adadin da ya kafa sabon matsayi.
Kafar yada labarai ta Reuters na ganin cewa, jigilar mutane a bikin bazara ba ma kawai ya bayyana saurin karuwar yawan mutanen da ake jigilarsu ba, har ma ya bayyana kwarin gwiwa da kuzarin da farfadowar tattalin arziki ke kawowa.
- Bikin Sabuwar Shekarar Sinawa Ta 2024: Maraba Da Shekarar Kwazo, Kuzari Da Nasara
- Li Qiang Ya Tattauna Da Kwararrun ‘Yan Kasashen Waje Dake Kasar Sin
Manazarta na ganin cewa, yawan kudaden dake shafar kayayyakin masarufi a bana zai zarce RMB Yuan triliyan 50, abin da ya ingiza bunkasuwar tattalin arzikin Sin sosai.
Saboda karuwar matsayin zamantakewar jama’a, Sinawa na iya tafiya ta hanyoyi da dama. Ban da wannan kuma, ana amfani da fasaha ta zamani don hidimar fasinjoji. An samu irin wannan sauyi ne dalilin bunkasuwar kimiyya da fasaha cikin sauri, a wani bangare na daban kuma, karuwar bukatun fasinjoji a dalilin bunkasuwar tattalin arziki da al’umma. Matakin da ya kai ga ci gaba da yin kirkire-kirkire a fannin ba da hidima don biyan bukatun kasuwa.
Duniya na iya ganin kuzarin kasar Sin ta yadda jigilar mutane ya kasance a bikin bazara. Shirin labaran duniya na Pakistan ya nuna cewa, jigilar mutane a bikin bazara ya bayyana kuzari da karfin kasar Sin na dogon lokaci, a matsayinta ta kasa ta biyu a duniya a bangaren karfin tattalin arziki. (Amina Xu)