Shugaban hukumar kula da harkokin aike da sakwanni ta kasar Sin Zhao Chongjiu ya yi bayani a gun taron aikin hukumar na shekarar 2025 a yau Laraba cewa, yawan sakwannin da aka yi jigilar aikewa a bara a nan kasar Sin ya kai biliyan 174.5, inda yawan kudin shiga da aka samu na aikin ya kai kimanin dala biliyan 191, adadin da ya karu da kashi 21% da kuma 13% cikin dari.
A cikin shekarar da ta gabata, hukumar ta yi kokarin fadada ayyukanta zuwa mabambantan kauyuka da tallafa wa hidimdimun zamanantar da yankunan karkara. Baya ga hakan, hukumar na kokarin kara fadada aikinta zuwa kamfanoni, ta yadda za a hidimtawa sana’o’in samar da kayayyaki bisa ci gaban kimiyya da fasaha.
Bugu da kari, domin kara kuzarin aikinta zuwa ketare da inganta raya cibiyar rarraba sakwanni, hukumar ta kafa cibiyoyin rarraba sakwanni a ketare 297 da dakunan adana sakwanni 333. Kazalika, ta karfafa ayyukan jigilar sakwanni ta layukan dogo 16 tsakanin Sin da kasashen Turai, da ta hanyoyin teku 25 tsakaninta da sauran sassan duniya daban daban.
An yi kiyasin cewa, a wannan shekarar da muke ciki, sana’ar za ta ci gaba da samun bunkasa ba tare da tangarda ba, inda yawan sakwannin da za a yi jigilarsu zai kai biliyan 190, kana adadin kudi da za a samu a wannan bangare zai kai kimanin dala biliyan 205. (Amina Xu)