Bayanai daga hukumomin kasar Sin sun nuna cewa, zuwa 6 ga wata, adadin masu kamuwa da cutar COVID-19 a kasar, ya sauka zuwa mataki mafi kankanta tun bayan 9 ga watan Disamban bara.
Bisa gwajin cutar da aka yi wa mutane, adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar ya kai miliyan 6.94 a ranar 22 ga watan Disamban 2022, wanda ya kasance mataki mafi koli. Daga nan kuma ya yi ta sauyawa, inda zuwa ranar 6 ga watan nan, ya sauka zuwa 9,000.
Babban jami’in yaki da annoba na cibiyar CDC ta kasar Sin Wu Zunyou, ya bayyana yayin wani taron manema labarai a yau cewa, abu ne mai wuya kasar ta kuma fama da wani zagaye na barkewar cutar a watanni masu zuwa, domin karfin garkuwar jikin mutane ya kai matsayin koli bayan sun warware daga cutar.(Faeza Mustapha)