A yau Talata ne kungiyar ingiza cinikayya ta kasar Sin, ta kira taron manema labarai, inda ta gabatar da “rahoton nazarin muhallin kasuwanci mai jarin waje na kasar Sin a rubu’i na 4 na shekarar 2022”, wanda ya nuna cewa, yawancin kamfanonin dake da jarin waje, sun gamsu da muhallin kasuwanci na kasar Sin.
Sakamakon binciken ya nuna cewa, kamfanoni masu jarin waje da yawan su ya kai kaso 90.22 bisa dari, sun gamsu da muhallin kasuwanci, da tsarin biyan haraji na kasar Sin, kuma kaso 88.26 bisa dari a cikin su, na nuna gamsuwa da ma’aunin shiga kasuwa da kasar Sin ta tsara.
Daga yunkurin zuba jari na kamfanoni masu jarin waje, kaso 9.78 bisa dari na kamfanoni masu jarin waje sun bayyana cewa, sun riga sun kara yawan jarin su a kasar Sin a rubu’in hudu na bara, kuma kaso 51.59 bisa dari sun ce sun zuba karin jari ne a kasar Sin da ribar da suka samu.
Haka zalika, yawancin kamfanoni masu jarin wajen da aka yi musu tambaya, sun nuna gamsuwarsu ga yanayin manyan ababen more rayuwar jama’a, musamman ma a fannin jigilar kayayyaki. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)