Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shirin raya birnin Fuzhou, fadar mulkin lardin Fujian dake gabashin kasar na tsawon shekaru 20 ne, a shekarar 1992 yayin da yake rike da mukamin sakataren kwamitin JKS na birnin. To ta yaya aka tabbatar da shirin? Xi ya fitar da dabarun aiwatar da wannan aiki na zurfafa kwaskwarima da habaka bude kofa ga kasashen waje, inda ya bayyana cewa, “Kwaskwarima ta ba mu kuzari, kuma bude kofa ga waje ya kara karfinmu.” Daga nan ne birnin Fuzhou ya cimma burin ci gaban tattalin arziki cikin sauri.
Ya zuwa shekarar 2010, an yi nasarar kammala shirin daga dukkan fannoni, GDPn Fuzhou ya karu daga kudin Sin Yuan biliyan 15 a shekarar 1992 zuwa biliyan 324.265 a shekarar 2010, adadin da ya karu da kaso 16 bisa dari, kana kudin shiga na mazauna garuruwan yankin ya karu har zuwa ninki 9, yayin da kudin shiga na mazauna kauyukan yankin ya karu da ninki 6.7. (Mai fassara: Jamila)