Wata babbar kotun Jihar Yobe da ke garin Pataskum ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya akan jami’in sojan nan Lance Corporal John Gabriel da ya hallaka fitaccen malamin Addinin Musuluncin jihar, Sheikh Bagoni Aisami.
Kotun ta kuma yanke hukuncin daurin shekaru 10 a gidan gyaran hali ga abokin aikin sojan mai suna Lance corporal Adamu Gideon da ya taimaka wajen aikata kisan.
- COP28: Sin Da Afirka Za Su Bunkasa Hadin Gwiwa A Fannin Raya Kananan Ayyukan Samar Da Makamashi Mai Tsafta
- Sin: Ya Kamata Kwamitin Sulhu Ya Kara Daukar Matakai Kan Lokaci Don Inganta Tsagaita Bude Wuta Da Kawo Karshen Yaki A Dukkan Fannoni
Da yake zartas da hukuncin, Alkalin kotun, mai shari’a Usman Zanna Mohammed, ya ce kotu ta sami John Gabriel da laifin kisan kai, shi kuma Adamu Gideon da laifin taimaka wa da ma hadin baki wajen aikata laifin.
Alkalin kotun ya ce mutanen biyu sun kasa tabbatarwa kotun cewa ba su da laifi, don haka aka yanke masu hukunci daidai da laifinsu.
In za a iya tunawa a watan Agustan bara ne aka kama jami’in soja bisa zargin yi wa sheikh Goni Aisami kisan gilla a wani wuri da ke yankin Karamar Hukumar Karasuwa a Jihar Yobe, kusa da garin Gashua bayan da malamin ya ragewa sojan hanya a motarsa daga garin Nguru.
A baya dai an yi ta jan kafa wajen gudanar da shari’ar da ta kai har sai da iyalai da daliban malamin da ma kungiyoyin fararen hula suka yi ta kokawa.