Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF) wadda ke kan gaba wajen rajin kare muradun al’ummar arewa ta kafa kwamiti 2 domin fito da tsare-tsare da manufofi na yadda za a tunkari matsaloli da kalubalen da yankin ke ciki a wannan lokacin.
Wannan na daga cikin shawarwarin da kwamitin aminttaun kungiyar suka cimma a taron da suka yi ranar 4 ga watan Satumba 2024.
- Janar Gowon: Tsohon Shugaban Kasa Mafi Tsawon Rai A Nijeriya Na Cika Shekara 90
- Hadarin Kwale-kwale A Kaiama: Gwamnan Jihar Kwara Ya Bayar Da Tallafin Naira Miliyan 100
An fitar da mambobin kwamitin ne bayan tattaunawsa da tuntuba inda aka fitar da masana masu kwazo da za su yi amfani da iliminsu wajen samar wa yankin arewa mafita a kan matsalolin da ake fuskanta arewa a halin yanzu.
Sanarwa da shugaban kwamitinm watrsa labarai na kungiyar, Farfesa Tukur Muhammad-Baba, ya sanya wa hannu ta bayyana cewa, an lura da tabarbarewar zamantakewa a tsakanin kabilu da al’ummun da ke yankunan arewacin kasar abin da kuma yake haifar da fadace-fadace wanda ya yi tarnaki ga zaman lafiya a yankin hakan kuma yana shafar kasa gaba daya.
An zabo ‘yan kwamitin ne domin su jagorancin karfafa juma da zaman lafiya a yankin arewa, sun kuma hada da Dakta Yayale Ahmed (Ajiyan Katagum) a matsayin shugaba sai Lawal wanda zai zama mataimakinsa.
Bangaren kwamitin da zai kula, da harkar tsaro na da alhakin tabbatar da ganin an samu tsaro a yankin arewa, musamman ganin yadda rashin tsaron ya haifar da manyan matsaloli ga al’umma yankin, an kuma nada tsohon shugaban rundunar sojojin Nijeriya Janar Abdulrahman Dambazau (mai ritaya) sai tsohon shugaban rundunar ‘yansandan Nijeriya a matsayin mataimaminsa.
Alhaji Bashir Dalhatu da Wazirin Dutse suka kaddamar da kwamitin a ranar 3ga watan Satumba da kuma ranar 1 ga watan Oktona 2 ana sa ran za su kammala aikinsu a tsakiyar watan Nuwamba na wannan shekarar.
Kungiyar ACF za ta tattauna a kan rahoton inda za ta kuma mika shwarwarinta ga gwamnonin yankin arewacin Nijeriya kafin a mika su ga gwamnatin tarayya wanda ita ce keda alhakin sarrafa jami’an tsaro a kasar nan.
Yadda Aka Kafa Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma
Bayan kwashe lokaci mai tsawo al’ummar yankin Arewa Maso Yammacin Nijeriya suna fafutukar ganin gwamnatin tarayya ta kafa Hukumar Bunkasa Yankin wanda yanzu ya fara zama koma baya wajen ci gaban tattalin arziki. Masana na ganin Kafa Hukumar Bunkasa Yankin Arewa maso Yammacin Nijeriyar dai, muhimmin mataki ne a kokarin kai dauki da tallafa wa wannan yanki. Matakin dai ya sanya murna har baka ga daukacin al’ummar yankin da suka kunshi jihohi bakwai, wadanda suka hada da Kaduna da Kano da Katsina da Jigawa da Zamfara da Kebbi da kuma Sokoto. Idan ba a manta ba Majalisar dokokin kasar ce dai ta taka muhimiyya rawa a wanan fafutuka, domin can ne aka fara aza girkin da ya haifar da samuwar wannan hukuma.
Tuni Shugaban kasa Bola TInubu ya nada mutum 7 wadanda za su jagoranci hukumar, sun kuma hada da Haruna Ginsau (Jigawa) a mastayin shugaba yayin da Farfesa Abdullahi Shehu Ma’aji (Kano) zai zama Manajin Darakta na hukjumar, sauran mabobin sun hada da Dr. Yahaya Namahe (Sokoto), Aminu Suleiman (Kebbi), Tijani Kaura (Zamfara), Abdulkadir Usman (Kaduna), Muhammad Wudil (Kano), Shamsu Sule (Katsina), da kuma Nasidi Ali (Jigawa).
Mataimakin Shugaban majalisar dattawan kasar nan Sanata Barau Jibril shi ne ya gabatar da kudurin da ya zama dokar kafa hukumar, ya bayyana fatan cewa kamar yadda Hukumar Raya Yankin Niger Delta da ke ayyukan gina hanyoyi da asibitoci da makarantu za a samu haka a yankin na Arewa maso Yammaci karkashin sabuwar hukumar.
Kokarin bunkasa ci gaban yankin da ke shan wahala musamman a fannin rashin tsaro na ‘yan bindigar da suka mayar da shi cibiyarsu, abin da ya haifar da mumunan koma baya ga al’ummarsa a fannin tsaro da tattalin arziki da ma yaran da ke fama da rashin abinci mai gina jiki. Masana na ganin akwai jan aiki a gaban hukumar musamman ganin yadda yankin yake fuskantar matsaloli masu yawan gaske. Sun kuma bayyana hanyoyin da hukumar za ta bi wajen tabbatar da cewa ta samu nasarorin da za su tada komadar ci gaban tattalin arzikin yankin baki daya. A kan hakan dattawan Arewacin Nijeriya suka bayyana cewa akwai bukatar a baiwa hukumar goyon baya domin za ta samar da abubuwan ci gaba a yankin. A wata zantawa da ya yi da wakilinmu, Farfesa Tukur Mohammed Baba, wanda shi ne Daraktan yada labarai na kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF) ya ce suna goyon bayan kafa ita hukumar musamman ganin yadda yankin Arewacin kasar nan yake fuskantar koma baya ta bangarori da dama. “Kamar yadda muke fadi ne, samar da hukumar nan alheri ne ga daukacin al’ummar Arewa saboda yankin Arewa yana bukatar irin wannan hukumar, idan ka duba zaka ga cewa al’ummar jihar suna fama da matsalar talauci da fatara da matsalar Rashin tsaro wanda yanzu ya yi mata katutu.
“Kashi 35 cikin 100 na al’ummar kasar nan suna rayuwa ne a yankin Arewa amma ga yadda yankin ya koma wanda a shekarun baya an San yankin da Noma da kasuwanci yanzu Komai ya tabarbare. Abin takaici yanzu Arewa ta fada cikin matsanancin hali inda mutane suke rayuwa cikin kunci da rashin tabbas na zaman lafiya. Idan ka dauki jihohin Katsina da Zamfara matsalar rashin tsaro ta zama barazana ga al’umma. “Mu ACF muna goyon bayan kafa wannan hukumar kuma sun kafa kwamitoci guda biyu na kwararru da za su fitar mana da abubuwan da Arewa take bukata domin baiwa hukumar. “Yanzu babban aikin da ke gaban hukumar shi ne samar da wata kasida Ko jaddawali a kan yadda za ta tafiyar da aikinta wajen samar da hanyoyin bunkasa ilimi da magance matsalar tsaro wanda idan ta fitar da jaddawalinta ina mai ganin za a samu saukin rayuwa a Arewa. “Ya zama wajibi hukumar da samar da hanyoyin dogoro da kanta kada ta rinka dogoro da abinda gwamnati za ta bata. Hakazalika, akwai bukatar gwamnati ta rinka tallafa wa hukumar da kudi masu yawa wanda haka zai taimaka mata wajen tafiyar da ayyukanta yadda ya kamata” Farfesa Tukur Mohammed Baba, ya ce lokaci ya yi da al’ummar yankin Arewa Maso yammacin kasar nan za su rungumi hukumar bisa ganin yadda yankin yake fama da mayuwacin hali yana mai cewa babu shakka hukumar za ta taka rawar gani wajen kawo ci gaba a yankin Arewa a dai dai lokacin da yankin ya fada cikin matsaloli da dama da suka dabaibaye ci gaban yankin.
Sai dai wasu masana suna ganin cewa kafa hukumar tamkar barnar kudi ne da bata lokacin musamman ganin cewa idan ana bukatar samar da abubuwan ci gaban Arewa ba sai an samar da wata hukuma ba. Dakta Usman Dalhatu masanin Diflomasiyya da kuma harkar tarihi a Arewacin kasar nan inda ya ce “maganar gaskiya kafa irin wannan hukuma bata da wata amfani duba da yadda duk wata hukuma da gwamnati yake kafawa basa iya samar da wani abun ci gaba ba face sun samu umarni daga gwamnatin” “Kawai an samar da hukumar ce domin bai wa wasu dama su samu kudi amma ba Wai ci gaban Arewa ba. Me su gwamnatocin yankin Arewa suke yi na kawo ci gaba a Arewa? Arewa Maso yamma bata bukatar samar da hukumar saboda idan aka ce an kafa wata hukuma shin menene ayyukan Gwamnatin jihohin suke yi na inganta rayuwar Al’ummar? Babu. Saboda haka ni anawa fahimtar bana goyon bayan kaf hukuma hasalima, babu wani abin za su tabuka illa satar kudade, shi yasa ni bana San magana Akan irin wadannan batutuwan domin babu gaskiya a tare da su”
Kunigiyar Kiristoci CAN reshen yankin arewa maso yamma ta soki yadda aka kasa samun Lrista ko daya a jerrin wadanda aka nada a matsayin mambobin hukumar raya yankin arewa maso yamma. Bayanin haka ya fito ne a wata sanarwa da shugaban kungiyar na yankin Sunday Oibe, ya sanya wa hannun aka raba wa manema labarai a Kaduna. Ya ce basu ji dadin wannan tsari na shugaban kasa ba. Ya nemi a gaggauta sake jerin sunayen a kuma tabbatar an samu wakilcin Kirista a ciki.
Haka kuma wasu gungun mata da suka hada da Asma’u Joda, Saudatu Mahdi, Maryam Uwais, Aisha Oyebode, Amina Salihu, Mairo Mandara, Kadriyya Ahmed, Fatima Akilu, Rabi Jimeta, da Habiba Mohammed sun fitar da sanarwa inda suke kalubalantar rashin mata a cikiin jerin mambobin hukumar raya yankin arewa maso yamma, sun ce hakan ba adalci ba ne. Sun nemi shugaban kasa ya gaggauta tabbatar da sanya mata a cikin jerin sunayen donmin tabbatar da adalci.