‘Yan gudun hijira a jihohin Borno da Binuwai na fama da matsanancin yunwa sakamakon alamun da ke nuna cewa manyan hukumomin Majalisar Dinkin Duniya na janye ayyukansu a Nijeriya saboda raguwar kudaden gudanar, kamar yadda bincike ya nuna.
Hukumomin dai su ne ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ayyukan jin kai (UNOCHA) da kuma hukumar samar da abinci ta duniya (WFP).
- Seyi Tinubu Ya Musunta Zargin Kamawa Da Bayar Da Cin Hanci Ga Shugaban NANS
- An Cafke Saurayi Bisa Zargin Yi Wa ‘Yar Budurwarsa Fyade A Bauchi
‘Yan gudun hijira a wasu sansanonin da ‘yan jarida suka ziyarta a jihohin Borno da Benuwai, sun bayyana fargabar cewa matakin da hukumomin samar da agajin gaggawa da kula bala’o’i biyu suka dauka na iya kara janyo kalubalen harkokin jin kai da ke fuskantarsu.
A sansanonin ‘yan gudun hijiran da ke Borno wadanda suka bar gidajensu sakamakon ta’addancin ‘yan kungiyar Boko Haram da kuma wadanda suke Benuwai da ya faru sakamakon hare-haren ‘yan bindiga a kauyuka daban-daban.
Ministan harkokin jin kai da rage radadin talauci na UNOCHA, Farfesa Nentawe Goshwe, ya sanar da yunkurin hukumar na ficewa daga Nijeriya. Ya shaida hakan ne a yayin taron kara wa juna sani kan tsarin da za a dauka a Nijeriya, wanda aka gudanar a cibiyar yaki da ta’addanci ta kasa, ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro a Abuja.
A cikin wata wasika da aka yada a shafin intanet na hukumar a ranar 11 ga Afrilu, shugaban hukumar ta UNOCHA, Tom Fletcher ya ba da sanarwar yanke ayyuka sakamakon karancin kudade na kusan dala miliyan 60 a shekarar 2025.
Hukumar ta ce za ta rage ayyukanta a Nijeriya, Kamaru, Kolombiya, Eritriya, Iraki, Libya, Pakistan, Turkiyya da Zimbabwe, da nufin ba da fifikon da maida cikakken karfi a sauran wuraren da take gudanar da ayyukanta.
Kazalika, ita ma hukumar samar da abinci ta duniya (WFP) a ranar 28 ga watan Maris ta yi gargadin cewa mutane miliyan 58 na cikin hadarin rasa taimakon ceton rai a cikin ayyukan 28 na ceto da hukumar take yi sakamakon raguwar kudade a cikin manyan masu ba da agaji.
Mataimakiyar Babban Darakta na WFP, Rania Dagash-Kamara kan hadin gwiwa da kirkire-kirkire, ta ce hukumar na fuskantar raguwar kudaden tallafin da kashi 40 cikin 100 a shekarar 2025, idan aka kwatanta da na bara.
Sai dai abu mafi muni, ‘yan gudun hijira sun nuna gayar damuwa bisa halin da suke ciki. Wasu ‘yan gudun hijira a Muna, Maiduguri, da ke Jihar Borno, sun shaida cewar tsawon watanni suna fuskantar matsalolin yunwa sakamakon janye ayyukan tallafi na abinci a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke jihar.
Shugaban sansanin Muna, Malam Abatcha Mustapha, ya ce ‘yan gudun hijira na cikin matsanancin rayuwa na yunwa kuma ba za su iya ci gaba da kasancewa ba tare da tallafin abinci ba.
“Mun samu kanmu a cikin tsaka mai wuya lokacin da suka daina kawo mana abinci, sai a ranar Sallah ne hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta kawo mana abinci. Mutanenmu suna cikin matsanancin yanayi. Muna zaman jiran umarni daga wajen gwamna domin komawa asalin gidajenmu a kananan hukumomi Dikwa da Mafa.”
Ya ce akwai ‘yan gudun hijira sama da mutane 44,000 a wannan sansanin kuma a shirye suke su koma gidajensu na asali domin ba karamar wahala suke sha a inda suke a halin yanzu ba.
Shugaban nakasassu a sansanin Abiso Kadi ya ce, “Tun daga lokacin da hukumar NEMA da sauran masu sa baki suka janye tallafin abinci na wucin gadi a wannan sansanin, rayuwa ta yi mana wuya, ba ni da aikin da zan yi a nan a matsayina na makaho, abin da na dogara da shi shi ne tallafin da hukumar NEMA ta bayar.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp