Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana, Alhaji Rabiu Garba-Kamba, a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Dandi/Arewa ta tarayya da ke Kebbi, wanda aka gudanar a ranar Asabar.
Jami’in zaben, Farfesa Aliyu Abdullahi-Turaki ne ya bayyana hakan a garin Kamba da ke karamar hukumar Dandi a ranar Lahadin da ta gabata.
- Zaben Cike Gurbin Makera: ‘Yan Takara Sun Yi Wa Liman Mubaya’a
- Hukuncin Zaben Adamawa: Na Rungumi Kaddara – Binani
Jami’in ya ce, Garba-Kamba na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 32,432, inda ya kayar da abokin hamayyarsa Abdullahi Umar-Kamba na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 31,858.
“Ni, Farfesa Aliyu Abdullahi-Turaki, ni ne Jami’in da na gudana da zaben cike-gurbi 2024 a mazabar Dandi/Arewa ta tarayya da aka gudanar a ranar 3 ga Fabrairu 2024.
“An gudanar da zaben kuma Rabi’u Garba-Kamba na APC bayan ya cika sharuddan doka, an bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara kuma a matsayin zababben dan majalisar wakilai ta kasa,” cewar Jami’in zaben.