Da yammacin yau Litinin ne jami’an sassa daban daban ciki har da na ma’aikatar cinikayyar kasar Sin, da na ma’aikatar harkokin wajen kasar, suka gana da manema labarai, game da shirin bude baje kolin hajojin shige da fice ko “Canton Fair” karo na 135, wanda zai gudana a birnin Guangzhou, hedkwatar lardin Guangdong na kudancin kasar Sin. Jami’an sun tabbatar da cewa, za a gudanar da baje kolin “Canton Fair” na 135 daga ranar 15 ga watan nan na Afrilu zuwa 5 ga watan Mayu.
A cewar mataimakin ministan kasuwancin kasar Sin Wang Shouwen, ayyukan da za a gudanar a bana yayin baje kolin sun dara na sauran lokutan baya, a fannin adadin kamfanonin da suka yi rajistar baje hajojin shige da fice, da sabbin mahalarta, da masu sayayya daga ketare da suka yi rajistar zuwa da dai sauransu.
Jami’in ya ce, a bana, yayin gudanar “Canton Fair”, ana sa ran baje hajojin Sin masu nasaba da manufar kasar ta bude kofa bisa matsayin koli a muhimman sassa 5, da suka hada da karuwar manyan kirkire-kirkire daga kamfanoni masu halarta, da fadadar dandalin yanar gizo, da nazarin matsayin ingancin hajoji, da goyon bayan daidaiton tsarin rarraba hajoji, da ci gaba da daga matsayin ayyukan baje kolin tare da managartan hidimomi. (Saminu Alhassan)