Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa, ta na shirin fara aiwatar da lamunin dalibai a watan Satumba ko Oktoban 2023.
Babban sakataren ma’aikatar ilimi ta tarayya, Andrew David Adejo ne ya bayyana hakan a Abuja a ranar Laraba yayin da yake zantawa da manema labarai kan kudirin dokar da shugaban kasa Bola Tinubu ya sanya wa hannu a kwanakin baya.
Shugaba Tinubu ya amince da kudirin lamunin dalibai domin cika alkawarin da ya dauka a lokacin yakin neman zabe.
Kudirin lamuni ga dalibai wanda shugaban majalisar wakilai ta 9, Femi Gbajabiamila ya jagoranta, ya tanadi lamuni marar ruwa ga daliban Nijeriya marasa galihu.
Dokar dai a takaice, ita ce samar da hanyoyin samun ilimi mai sauki ga ‘yan Nijeriya marasa galihu ta hanyar bayar da lamuni mara ruwa daga asusun lamuni na ilimi na Nijeriya, in ji babban sakataren.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp