Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire, JAMB, a karshen taronta a ranar Talata, ta fitar da wasu manyan ranakun gudanar da ayyukanta na shekarar 2023.
Sakamakon haka, Hukumar ta amince da fara rajistar jarrabawar shiga makarantun gaba da Sakandire ta shekarar 2023 (UTME) daga ranar Asabar 14 ga Janairu zuwa Talata 14 ga Fabrairu, 2023.
Za a fara rajistar DE daga ranar Litinin, 20 ga Fabrairu zuwa Alhamis, 20 ga Afrilu, 2022.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp