Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, ya ce da yiyuwar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta kirkiro wasu sabbin ma’aikatu da za su zama kari kan wadanda ake da su.
Femi ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis a Abuja, inda ya ce bayan jerin ministoci 28 da Tinubu ya gabatar, zai kuma sake aikewa da sunayen mutum 13 nan gaba kadan.
- Hamza Abara Ya Zama Sabon Kocin Niger Tornadoes
- Gwamman Zamfara Ya Karrrama Hajiyar Da Ta Tsinci Dala 80,000 A Saudiyya
Ya ce, ministocin da aka gabatar sai da suka tsallake tantancewar shugaban kasa da kansa.
Ya ce ba ya ga sunan mutum 28 da Tinubu ya gabatar a matsayin ministoci, zai kuma sake aikewa da kashi na biyu na ministocin da suka kunshi sunayen mutum 13.
“Kamar yadda kuka sani kwanaki 60 da rantsuwa, kamar yadda yake kunshe cikin kundin tsarin mulki. Ya cika ka’idar ya gindaya ta hanyar tura sunayen mutum 28 a yau.
“Kamar yadda aka karanta cikin wasikarsa a gaban majalisar dattawa, akwai karin sunayen da za a gabatar, babu tabbacin su nawa ne amma wakila za su haura 12, za a tura sunayen ga majalisar dattawa nan da ‘yan kwanaki.”
Kamfanin Dillacin Labarai (NAN) ta ruwaito cewa Gbajabiamila ne ya gabatar da jerin sunayen ministocin da Tinubu ya zaba kuma shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya karanta a majalisar.
Ministocin da aka zaba 28 su ne: Abubakar Momoh, Yusuf Maitama Tuggar, Ahmed Dangiwa, Hannatu Musawa, Chif Uche Nnaji, Dokta Betta Edu, Dokta Doris Aniche Uzoka, David Umahi da Nyesom Wike.
Sauran su ne Badaru Abubakar, Nasiru Ahmed El-Rufai, Ekperipe Ekpo, Nkeiruka Onyejocha, Olubunmi Tunji Ojo, Stella Okotette, Uju Kennedy Ohaneye, Mista Bello Muhammad Goronyo, Mista Dele Alake, da Mista Lateef Fagbemi.
Akwai kuma Mista Muhammad Idris, Mista Olawale Edun, Mista Waheed Adebayo Adelabu, Misis Iman Suleiman Ibrahim, Farfesa Ali Pate, Farfesa Joseph Utsev, Sanata Abubakar Kyari, Sanata John Enoh, da kuma Sanata Sani Abubakar Danladi.