Shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 25 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen Sin da Afirka ta Kudu, inda aka shiga lokaci mai kyau na raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, wadda ta kasance daya daga cikin muhimman huldodi tsakanin kasashe masu tasowa.
Babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG, da kamfanin rediyo na Afirka ta Kudu sun yi hadin gwiwar tsara shirin gaskiya mai taken “Shekaru 25 na sada zumunta da hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka ta Kudu”.
- Sojojin Ruwan Kasar Sin Sun Shafe Shekaru 15 Suna Aikin Tabbatar Da Tsaro A Mashigin Tekun Aden Da Gabar Tekun Somaliya
- Jirgin Ruwa Mai Binciken Teku Na Farko Na Kasar Sin Ya Gwada Yin Aiki Cikin Nasara
An fara shirin daga ziyarar aikin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi a Afirka ta Kudu karo na 4, da nuna nasarorin hadin gwiwar kasashen biyu a fannonin harkokin diplomasiyya, da tattalin arziki, da al’adu.
Shirin ya shaidawa masu kallo na Sin da Afirka ta Kudu yadda sassan 2 suka yi hadin gwiwa da samun moriyar juna, da sada zumunta a tsakanin jama’ar kasashen biyu, da kuma yin mu’amalar al’adunsu baki daya. (Zainab Zhang)