Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce sama da naira tiriliyan 1 da za a tara daga janye tallafin wutar lantarki za a sake zuba su ne wajen inganta wutar lantarki, kiwon lafiya, da ilimi ga ‘yan Nijeriya.
Da yake jawabi a matsayin babban baƙo na shahararren shirin Rediyo Nijeriya na Kaduna mai suna ‘Hannu Da Yawa’ a ranar Asabar a Kaduna, Idris ya ce a kusan kashi 40 na tallafin wutar lantarki, kashi 15 ne kawai masu amfani da wutar lantarki ke amfana wanda ya ƙunshi mawadata da gungun masana’antu, waɗanda ke jin daɗin wutar lantarki na kusan awanni 20.
- Mene Ne Dalilin Da Ya Sa Japan Ke Daukar Wasu Matakan Da Ka Iya Haifar Da Hadari?
- Yanzu-yanzu: Hatsaniya Ta Kaure Tsakanin Sojoji Da Matasa A Gashuwa
Ya ce, “Yana da muhimmanci a jaddada cewa kuɗaɗen da za a ajiye daga janye tallafin wutar lantarki, za a sake zuba su ne wajen inganta samar da wutar lantarki a faɗin ƙasar nan da inganta sauran muhimman ayyukan jama’a kamar kiwon lafiya da ilimi. Kusan kashi 85 cikin ɗari na al’ummar da ke cikin sabon tsarin samar da wutar lantarki har yanzu suna samun tallafin.”
Ministan ya ce sabuwar dokar samar da wutar lantarki da Shugaban Ƙasa Tinubu ya sanya wa hannu ta ƙara ƙarfafa tsarin gudanar da ayyukan Hukumar Kula Da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC) tare da bai wa hukumar damar sanya wa kamfanonin rarraba wutar lantarkin (DISCOs) tsauraran takunkumi kan laifukan da suka shafi kuɗi da samar da wutar ga masu amfani.
Idris ya kuma bayyana cewa kwamitin da Shugaban Ƙasa ya kafa domin duba tsarin tafiyar da Shirin Zuba Jarin Jama’a na Ƙasa ya gabatar da rahotonsa domin share fagen sake gudanar da shirye-shiryen, wanda zai bayar da tallafin kuɗi naira 25,000 ga talakawa miliyan 15 da magidanta masu rauni na tsawon watanni uku a tsakanin sauran ayyukan.
Ministan, wanda ya yi amfani da wannan dandali wajen kawar da maganar da wasu ke yi cewa wai gwamnatin Tinubu na shirin cutar da arewacin ƙasar nan, ya jaddada cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da zuba kuɗaɗe wajen bunƙasa ayyuka a Arewa.
Ya yi nuni da cewa gwamnatin ta faɗaɗa noman alkama, shinkafa, rogo, da masara, a ƙarƙashin Shirin Noman Rani zuwa kadada 500,000 na gonaki.
Ya ce: “Shugaban Ƙasa ya umarce mu da mu fito mu ji halin da al’umma ke ciki, mu kawo masa rahoto. Mun je Dutse, Auyo, da Haɗeja, kuma mun tattauna da manoma game da nasarorin noman rani a waɗannan yankuna”.
Idris ya bayyana jin daɗin sa kan yadda a yanzu Jihar Kebbi ta zama cibiyar noman tumatur da sarrafa tumatur a ƙasar nan ta hanyar haɗin gwiwa da wani babban kamfanin sarrafa abinci mai suna GB Foods, wanda ya kafa wata masana’anta domin noman tumatur.
Ya ce manoma da dama, waɗanda galibin su mata ne, yanzu haka su na noman tumatur a Jihar Kebbi, saboda yanayin da ake samu da kuma tallafi daga GB Foods, wanda ya nuna matuƙar jajircewa wajen yin kasuwanci a Nijeriya.