An kira taron manema labarai game da zama na biyu na majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar Sin (CPPCC) karo na 14 da yammacin yau Lahadi 3 ga watan Maris, inda kakakin taron, Liu Jieyi ya gabatar wa kafafen yada labaran gida da na waje abubuwan da suka shafi taron, tare da amsa tambayoyi.
Kakakin ya ce, za’a kaddamar da zama na biyu na majalisar CPPCC karo na 14 da misalin karfe 3 na yammacin gobe Litinin, a babban dakin taron jama’a dake Beijing, wanda za’a rufe shi a safiyar ranar 10 ga watan, inda za’a takaita ayyukan majalisar CPPCC na shekarar da ta gabata, da tsara shirye-shiryen ayyukan bana. Majalisar za kuma ta kara tallata kyawawan al’adunta, da bude sabon babi ga ayyukanta a sabon zamanin da muke ciki.
Yayin da yake amsa tambayoyin ‘yan jaridun gida da waje, Liu Jieyi ya ce, batun tattalin arziki na jawo hankalin membobin majalisar CPPCC sosai, kana daya ne daga cikin muhimman batutuwan da za’a tattauna a kai. A ganin membobin, a shekarar da ta shude, a karkashin jagorancin kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wanda Xi Jinping shi ne jigonsa, tattalin arzikin kasar ya murmure, kana an yi nasarar cimma babban burin bunkasuwar tattalin arziki da kyautatuwar zaman rayuwar al’umma. A shekarar da muke ciki, CPPCC za ta ci gaba da bada taimako ga raya tattalin arzikin kasa, da gudanar da shawarwari kan muhimman batutuwan tattalin arziki ta hanyoyi daban-daban, da bayar da kyawawan nasihohi, da tattaro ra’ayoyin mutanen bangarori daban-daban, a wani kokari na bayar da gudummawa ga sha’anin samar da ci gaba mai inganci. (Murtala Zhang)