Jami’in ma’aikatar sufuri ta kasar Sin Li Guoping ya bayyana cewa, gwamnatin kasar za ta kara samar da goyon baya ga sana’ar kera motoci da fasahohin zamani dake amfani da sabbin makamashi.
Jami’in ya bayyana haka ne bayan rufe babban taron motoci masu amfani da sabbin makamashi na duniya a jiya Lahadi.
Li Guoping yana mai cewa, mataki na gaba shi ne nazari da tsara tsarin rage fitar da sinadarin carbon, kuma za aiwatar da manufar bayar da tallafi don yayata amfani da motoci masu amfani da sabbin makamashi.
Li Guoping ya nuna cewa, ma’aikatar sufuri za ta gudanar da ayyukan da suka shafi motoci masu amfani da sabbin makamashi da fasahohin kwaikwayon tunanin bil Adam, da karfafa nazarin muhimmiyar fasahar sufuri mai basira da sufuri mai kiyaye muhalli, don samar da tallafin kimiyya da fasaha. (Mai fassarawa: Safiyah Ma daga CMG Hausa)