Wata babbar kotun Yola da ke Jihar Adamawa ta yanke wa wasu mutane biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamakon samun su da laifin kisan kai.Â
Mai shari’a Kaynson Lawanson ne, ya yanke wa mutanen hukuncin, a ranar Talata.
- Yanzu-yanzu: Wani Abu Ya Fashe A Tashar Iskar Gas A Ibadan
- Da Dumi-dumi: Tinubu Ya Gana Da Shugabannin Tsaro Kan Karuwar Rashin Tsaro
Da yake yanke hukuncin, Mai shari’a Lawanson ya ce, “Hukuncin da kotu ta yanke muku za a rataye ku ko kuma kisa ta hanyar allura. Ubangiji ya yi muku rahama.”
Masu gabatar da kara sun bayyana cewa wadanda aka yanke wa hukuncin sun hada baki tare da yi wa wani dan acaba mai suna Algoni Muhammed fashi.
Bayan sun yi masa fashi suka kwace masa Kekenapep dinsa, sannan suka kashe shi tare da karya wuyansa a ranar 4 ga Afrilu, 2022.
Daga nan suka tafi da babur din suka sayar da shi.
Alkalin kotun ya ce yana fatan hukuncin ya zama izina ga wasu masu aikata irin wannan mummuna laifi.