Babban Bankin Duniya ya ce akwai yuyuwar ‘ƴan Nijeriya da Angola za su fuskanci ƙarin hauhawar farashin mafi tsanani kan Kayan abinci da wutar lantarki da rashin fetur a kasashen biyu.
Wani rahoto da BBC ta wallafa ya ce, waɗannan matsaloli za su zo ne a yayin da farashin ɗanyen fetur ya kai kai dala 120 duk ganga ɗaya, lamarin da ake sa ran zai amfani waɗannan ƙasashen da dama su ne manyan ƙasashen Afirka da suka fi samar da fetur.
A wani rahoto da Babban Bankin Duniya ya fitar a ƙarshen mako, ya ce “A ƙasashen kudu da hamadar Sahara da dama, za a samu hauhawar farashi da da ƙarancin wutar lantarki da ƙarancin abinci da man fetur.”
Wannan batu na zuwa ne a daidai lokacin da dama Nijeriya ke fuskantar matsannacin hauhawar farashi da ƙarin samun layuka a gidajen mai a faɗin ƙasar.