Babban daraktan ma’aikatar ilimi ta kasar Ghana, Divine Yao Ayidzoe, ya ce nan bada jimawa ba, za sanya Sinanci cikin manhajar ilimi ta kasar.
Daraktan ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi yayin wani taron da aka shiriya jiya a cibiyar nazarin harshen Sinanci ta Confiscius dake jami’ar Cape Coast ta Cape Coast, babban birnin yankin tsakiyar Ghana.
Da yake jadadda karuwar muhimmancin koyon harshen Sinanci, baya ga harshen da kasar ke amfani da shi a hukumance, daraktan ya ce bisa la’akari da fadadar tattalin arzikin kasar Sin zuwa na biyu mafi girma a duniya, hakika wadanda suka koyi Sinaci sun yi sa’a matuka.
Ya kuma bukaci dalibai su yi amfani da damar wajen koyon Sinaci da al’adun Sinawa, domin shiryawa gaba.
A nasa bangaren, Ou Yamei, daraktar cibiyar Confiscius, ta bayana cewa, shirin sanya Sinanci cikin manhajar ilimi ta kasar Ghana, ya cancanci yabo matuka. (Fa’iza Mustapha)