Hukumar kula da yanayin sararin samaniya ta Nijeriya (NiMet) ta yi hasashen tsawa da mamakon ruwan sama daga ranar Lahadi zuwa Talata a fadin kasar.
An fitar da hasashen yanayi na NiMet ne ranar Asabar a Abuja, inda aka yi hasashen za a yi tsawa a ranar Lahadi da ruwan sama a wasu sassan jihohin Adamawa, Taraba, Borno, Kebbi, Kaduna, Gombe, da Yobe da safe.
- Wane Tasiri Sabbin Karfin Ci Gaban Kasar Sin Za Su Yi Ga Duniya?
- Wakilin Sin A MDD Ya Bukaci Sassan Kasa Da Kasa Da Su Bunkasa Hadin Gwiwa Tare Da Kungiyar SCO
A washegari, ana sa ran za a yi tsawa a duk fadin yankin Arewa. Ana sa ran ruwan sama a yankin Arewa ta tsakiya da safe.
An yi hasashen tsawa mai matsakaicin karfi tare da ruwan sama a sassan babban birnin tarayya, Filato, Benuwe da Kogi.
Inda kuma ake sa ran samun ruwan sama na tsaka-tsaki da safe a sassan Ondo, Ogun, Edo, Bayelsa, Cross River, Rivers, Akwa Ibom da Delta.
Saboda haka, NiMet ta shawarci mazauna yankunan da su guji wuraren da ambaliyar ruwa ta fi kamari domin akwai yiwuwar ambaliya a manyan biranen kasar sakamakon mamakon ruwan sama.