• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Za A Shiga Mummunar Damuwa A Gaza Idan Ba Ku Dauki Mataki Ba – Gargadi Ga Majalisar Tsaro Ta MDD

by Sulaiman
2 years ago
Gaza

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya (MDD), Antonio Guterres, ya rubuta wasiƙa ga kwamitin tsaro na majalisar, inda ya nemi ƴan kwamitin su taimaka don kauce wa mummunar annoba a Gaza.

“Yayin da ake fuskantar shiga bala’in rasa agaji a Gaza, ina neman Kwamitin ya taimaka wajen kauce wa afkuwar bala’i, kuma ya nemi a tsagaita wuta don kai agaji,” in ji Guterres a cikin wani saƙo da ya wallafa ranar Laraba.

  • Ana Iya Fahimtar Tattalin Arzikin Kasar Sin Daga Mahanga Mai Fadi
  • Iwobi Ya Jefa Kwallo 2 Yayin Da Fulham Ta Lallasa Forest Da Ci 5-0

Cikin wasiƙar da ya rubuta, Guterres ya nanata cewa yanayin na ƙara ƙazancewa cikin sauri, ta yadda ba za a iya gyara wa Falasɗinawa komai ba daga baya da kuma tsaron yankin.

Ya ƙara jaddada buƙatar tsagaita wuta saboda yadda lamarin ke ƙara ƙazancewa a Gaza, da kuma neman zaman lafiya a yankin.

Guterres yace “wannan ne karon farko da nake ɗaukar irin wannan mataki tun bayan zama na sakatare janar na MDD a 2017”.
Bugu da kari, Guterres ya ce alhakin ƙasashen duniya ne su shiga tsakani domin kawo ƙarshen yaƙin.

LABARAI MASU NASABA

Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

Ta’addanci Ba Zai Yi Nasara Ba A Ƙasarmu — Tinubu

Ya yi amfani da ayar doka ta 99 ta MDD, wadda ta ba shi damar jawo hankalin Kwamatin Tsaro kan “duk wani batu da yake ganin zai iya barazana ga zaman lafiyar duniya da tsaro”.

Guterres wanda ke kira da a “tsagaita wuta cikin gaggawa” tun daga ranar 18 ga Oktoba – ya kuma bayyana “mummunan wahalar dan Adam, lalatar jiki da kuma raunin gaba daya a duk fadin Isra’ila da yankunan Falasdinawa da ta mamaye.”

A yayin da ake ci gaba da kai hare-haren, Mista Guterres ya ce ya yi imanin lamarin “na iya kara tsananta barazanar da ake fuskanta na wanzar da zaman lafiya da tsaron kasa da kasa.”

ya yi gargadin cewa zaman lafiyar jama’a a Gaza na iya wargaje nan ba da jimawa ba a daidai lokacin da tsarin ayyukan jin kai ke durkushewa.

“Halin da ake ciki yana kara tabarbarewa zuwa wani bala’i wanda zai iya haifar da tasiri ga falasdinawa gaba daya da kuma zaman lafiya da tsaro a yankin,” in ji shi.

Ya jaddada cewa idan aka tsagaita wuta, akwai fatan zaman lafiya da kuma damar kai agajin taimako.

Amma duk da haka, jakadan Isra’ila na Majalisar Dinkin Duniya, Gilad Erdan bai amince da kiran da Mista Guterres ya yi kan mataki na ayar doka ta 99 ta MDD ba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 
Manyan Labarai

Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

November 6, 2025
Gwamnatin tarayya
Labarai

Ta’addanci Ba Zai Yi Nasara Ba A Ƙasarmu — Tinubu

November 6, 2025
Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari
Ra'ayi Riga

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

November 6, 2025
Next Post
An Fara Aiki Da Dakin Binicke Mafi Zurfi Da Girma A Duniya Dake Karkashin Kasa A Kasar Sin

An Fara Aiki Da Dakin Binicke Mafi Zurfi Da Girma A Duniya Dake Karkashin Kasa A Kasar Sin

LABARAI MASU NASABA

Manufofin Sin Na Yaki Da Sauyin Yanayi: Gani Ya Kori Ji

Manufofin Sin Na Yaki Da Sauyin Yanayi: Gani Ya Kori Ji

November 6, 2025
Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Ingantaccen Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Tashar Ruwa Ta Hainan

Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Ingantaccen Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Tashar Ruwa Ta Hainan

November 6, 2025
Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

November 6, 2025
A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

November 6, 2025
Gwamnatin tarayya

Ta’addanci Ba Zai Yi Nasara Ba A Ƙasarmu — Tinubu

November 6, 2025
Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

November 6, 2025
Za Mu Ƙara Ƙaimi Wajen Kai Wa ‘Yan Bindiga Hare-Hare Ta Sama – Hafsan Sojin Sama

Za Mu Ƙara Ƙaimi Wajen Kai Wa ‘Yan Bindiga Hare-Hare Ta Sama – Hafsan Sojin Sama

November 6, 2025
Garkuwa: Sarkin Gobir Ya Bukaci Agajin Gaggawa Daga Gwamnatin Sakkwato

An Kama Wani Mutum Kan Zargin Kashe Matarsa A Sakkwato

November 6, 2025
Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Don Karɓo Rancen N1.15trn Don Cike Giɓin Kasafin Kuɗin 2025

November 6, 2025
Jirgin Ƙasa Ya Murƙushe Direban Adaidaita Sahu Da Fasinja A Jos

Jirgin Ƙasa Ya Murƙushe Direban Adaidaita Sahu Da Fasinja A Jos

November 6, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.