A yayin da ake kan shari’a da wani kamfanin hada-hadar kuɗaɗen kirifto mai suna Binance kan zargin karya doka wajen hada-hadar, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce za a bi dukkan matakan doka don tabbatar da adalci a shari’ar.
A cikin wata sanarwa da mataimakin Ministan na musamman kan yaɗa labarai, Rabi’u Ibrahim, ya fitar a ranar Laraba, a madadin Ministan ya bayyana cewa, ana bin dukkan ƙa’idojin doka wajen gudanar da shari’ar.
- Da Dumi-Dumi: Edun Ya Mika Wa Tinubu Sabon Tsarin Mafi Karancin Albashin Ma’aikata
- Kotu Ta Bayar Da Umarnin Aike Wa Ganduje Da Wasu Sammaci Ta Wasu Hanyoyi Daban
Ya ce, “A kowace gaba, ana bin doka da oda, kuma masu gabatar da ƙara su na da yakinin samun nasara a shari’ar, ganin irin ƙwararan shaidu da hujjoji da aka tattara.
“Binance zai sami damar kare kansa a kotu game da waɗannan manyan tuhume-tuhume na almundahanar kuɗi da ya tafka a Jamhuriyyar Tarayyar Nijeriya. Za a ci gaba da sauraren ƙarar a ranar 20 ga Yuni, 2024.”
Idris ya bayyana cewa, an bai wa Binance – wanda ke kare kansa a shari’ar, duk wata dama da duk wata kulawar da ta dace, sakamakon samun kula ta ofishin jakadanci da diflomasiyya da aka saba da su, ya ƙara da cewa, alƙalin da ke shari’ar ya bayar da gamsasshen bayanin cewa, an hana beli ne ga jami’in kamfanin saboda akwai yiwuwar ya tsere, ganin cewa, wanda ake tuhumarsu tare ya tsere, kuma yanzu haka ‘Yansandan Ƙasa da Ƙasa (Interpol) suna farautarsa.