Sabbin jami’an ‘yan sanda 10,000 da aka yaye, za a tura kowanna su ne kananan hukumominsu na asali domin gudanar da aikin dan sanda mai inganci a fadin kasar nan.
Babban Sufeto Janar na ‘yan sanda, IGP, Alkali Baba Usman ne ya bayyana hakan a jiya Laraba a yayin bikin kaddamar da fareti na ‘yan sanda a Ilorin, jihar Kwara.
Usman ya ce daukar jami’an ‘yan sandan wani bangare ne na yunkurin gwamnatin tarayya na tabbatar da ingantattun ma’aikata domin yakar kalubalen tsaron kasar nan.
Shugaban ‘yan sandan ya ce Mutum 11 ne kawai ba su samu damar yin bikin ba sabida matsalar rashin lafiya.
Usman wanda ya samu wakilcin mataimakin babban sufeton ‘yan sandan Nijeriya, AIG, Ede Ayuba, ya ce rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta shirya daukar ‘yan sanda 10,000 duk shekara domin cike gibin da ake fama da shi na karancin jami’an ‘yan sanda a kasar.