Kafin shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci taron koli na kasar Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya karo na 2 a birnin Astana na kasar Kazakhstan, za a watsa shirin “Bayanan magabata dake jan hankalin Xi Jinping” a kafofin watsa shirye-shirye da dama na kasashen biyar, shirin da kafar CMG ta kasar Sin ta tsara shi.
Ana sa ran watsa shirin tun daga ranar Litinin 16 ga watan nan a kasashen Kazakhstan, da Kyrgyzstan, da Tajikistan, da Turkmenistan da kuma Uzbekistan.
Rahotanni na cewa, a ‘yan kwanakin baya-bayan nan, kafofin watsa shirye-shirye da dama dake kasashen Asiya da Turai, sun gudanar da gwajin watsa shirin, wanda sassa daban daban ke ta doki, da dakon zuwan lokacin nuna cikakkensa. (Saminu Alhassan)